
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta gargadi yan siyasa kan kaucewa yakin neman zaben 2027 har sai ta bayar da izinin yin hakan.
Sakataren yada labaran shugaban hukumar, Rotimi Oyekanmi ne ya bayyana gargadin ga manema labarai, tare da cewa har yanzu INEC bata fitar da lokacin yakin neman kuri’u ga jam’iyyu ba.
Oyekanmi ya ce hukumar zaben ta lura cewa wasu jam’iyyu sun fara yada hotunan yan takara na zaben 2027 gabanin jiran sanar da lokacin fara gangamin daga hukumar wanda hakan ya sabawa doka.
Ya kara da cewa sashi na 94 (1) na dokar zabe ta 2022 ya ce jam’iyyun siyasa za su fara gangamin neman kuri’u ne kwana 150 kafin ranar zabe da kuma dakatar da shi sa’oi 24 kafin fara jefa kuri’a.