Hukumar Zaɓe mai zaman kanta ta Ƙasa (INEC) ta ce jam’iyyun ADC, PDP da LP ba za su shiga zaɓen cike gurbi na ranar 21 ga Fabrairu a Jihar Rivers ba.
za’a gudanar da zaɓen ne a mazaɓun Ahoada East 2 da Khana 2, bayan ayyana kujerun a matsayin babu kowa sakamakon murabus ɗin Edison Ehie, wanda gwamna Siminalayi Fubara ya naɗa a matsayin shugaban ma’aikatan fadar gwamnati da kuma rasuwar Dinebari Loolo.
Kwamishinan Zaɓen jihar Rivers, Gabriel Yomere, ya ce jam’iyyu bakwai AA, APC, APN, BP, NNPP, YPP da ZLP ne aka tantance domin shiga zaɓen.
Ya bayyana cewa an cire PDP saboda rashin gudanar da zaɓen fidda gwani, LP saboda tana cikin shari’a, yayin da ADC ta gaza ɗora sakamakon fidda gwani a kan lokaci.
INEC ta tabbatar da cewa ta shirya tsaf domin gudanar da zaɓen cikin gaskiya da adalci, inda ta jaddada cewa ma’aikatanta ne kaɗai za su jagoranci aikin zaɓen.
