Sarkin Kano na 15 kuma uban Jami’ar Calabar, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya shawarci daliban da suka kammala karatu da su fifita kyawawan ɗabi’u da halaye fiye da takardun shaidar karatu, yana mai cewa ilimi ba ya cika sai da tawali’u da mutunta jama’a.
Sarkin ya bayyana hakan ne a wajen bikin yaye daliban jami’ar karo na 38 da aka gudanar a filin wasa na Abraham Ordia, inda ya jaddada cewa hikima ta gaskiya tana bayyana ne ta hanyar nutsuwa, ladabi da kyakkyawar mu’amala, ba wai ta hanyar nuna takama ko fariya da ilimi ba.
Ya ce, “Akwai waɗanda suka samu manyan takardun karatu, amma idan suka yi magana za ka gane ilimin ya zama nauyi kawai a kansu. Ilimi na gaskiya yana bayyana ne cikin natsuwa, tawali’u da halaye nagari.”
Ya gargadi masu ilimi da su guji girman kai, yana mai cewa masu ilimi na gaskiya ba sa neman a yaba musu ta hanyar fushi ko nuna takama.
A cewarsa, ilimi ya kamata ya gyara ɗabi’ar mutum maimakon ya lalata ta, yana kira ga daliban da su tabbatar ilimin da suka samu ya zama mai amfani ga al’umma.
Ya ce “Ku sa iliminku ya zama haske ga mutane, ba abin tsoro ba. Maganganunku su nuna hikima, ba hayaniya ba,” in ji shi.
Shi ma da yake jawabi, shugaban Jami’ar Calabar, Offiong Efanga, ya bayyana bikin yaye daliban a matsayin wani babban mataki a tafiyar ilimi ta jami’ar.
Ya ce dalibai 743 ne suka samu digirin digirgir na biyu (Masters), yayin da dalibai 9,173 suka kammala digirin farko, sannan 152 suka samu difloma.
Haka kuma, ya ce dalibai 52 ne suka kammala da sakamakon daraja ta farko (First Class), yana mai ƙara da cewa jami’ar za ta ɗauki wasu daga cikin fitattun daliban domin ba su aiki a muhimman sassa na jami’ar.
