Hukumar Hana Safarar Bil’adama Ta Kasa (NAPTIP) reshen jihar Kano ta kama wata mata a bisa zargin safarar wasu mata 7 zuwa kasar waje.
Mai magana da yawun hukumar Muhammad Habib ne ya bayyana haka inda a wata sanarwa da ya fitar.
“Hukumar ta samu nasarar hakan ne a wani sumame da ta kai wani gida a unguwar Rijiyar Zaki, sakamakon wasu bayanan sirri da ta samu.
“Ana amfani da gidan ne wajen ajiye matan da ake kokarin tura wa Saudiyya, binciken farko ya nuna cewa biyu daga cikin wadanda aka ceto ‘yan kasar Niger ne, yayin da biyar ‘yan Najeriya ne”.
“Kowacce daga cikinsu an dora musu bashin Naira miliyan goma (₦10,000,000) wanda dole ne su biya bayan sun isa kasar ta Saudiyya domin aikatau”.
Hukumar ta ce, sauran mutanen da ke da hannu a safarar sun tsere, kuma ana cigaba da bincike domin cafke su.
