
Hukumar Tace Fina-Fine da Dab’i ta Jihar Kano ta tabbatar da kama fitaccen mai shirya fina-finai, Umar UK, bisa zargin karya dokokinta.
Kakakin hukumar Abdullahi Sani Sulaiman ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya aikawa Premier Radio a ranar Alhamis, ya kuma bayyana kalubalantar ikon hukumar a matsayin babban dalilin ya sa ta kama shi.
“Umar UK ya wallafa wani bidiyo a shafinsa na sada zumunta yana kalubalantar ikon hukumar.
Bidiyon da aka wallafa yana ɗauke da ikirarin cewa babu wanda zai hana shi sakin finafinansa ba tare da tantancewa ba, lamarin da hukumar ta ɗauka a matsayin cin zarafi da karya doka”. In ji sanarwar.
Hukumar ta kuma musanta zargin da wasu ke yi mata na cewa tana zagon ƙasa ga masu goyon bayan gwamnati, inda ta ce a baya ma ta gurfanar da wasu manyan ‘yan masana’antar Kannywood bisa laifin karya dokokinta.
A kwanan baya hukumar ta dakatar da nuna wasu finafinai masu dogon zango ciki har da fim din Garwashin na Umar UK sai an tantance su, matakin da ya jawo ce-ce-ku-ce daga wasu mambobin Kannywood musamman masu goyon bayan darikar Kwankwasiyya.
Wasu daga cikinsu sun zargi shugaban hukumar Abba Almustapha da amfani da ikon sa wajen hana masu hidima wa gwamnati damar fitar da finafinai.