Daliban sun kamala karatunsu na digiri na biyu a fannoni daba-daban daga daya daga cikin manyan jami’oin kasar
Gwamnan Kano tare da mataimakinsa da kuma sauran jami’an gwamnati ne suka tarbi daliban a Filin Jirgin Saman Malam Aminu Kano, ranar Asabar.
Daga bisani, an shirya musu wani taro na musamman a Fadar Gwamnatin jihar don murnar nasarorin da suka samu a karatun nasu.
Gwamna Abba ya ce daliban da suka karanci fannin injiniyanci da likitanci za su samu aiki kai-tsaye.
Gwamnan, ya kuma gode wa iyayen daliban kan amincewarsu da gwamnati, tare da yaba wa tsohon gwamnan jihar Rabiu Musa Kwankwaso, bisa kaddamar da shirin tallafin karatu zuwa kasashen waje.
Ya kuma ce, mutane da dama ciki har da wasu daga cikin kwamishinoninsa sun ci gajiyar shirin a baya.
Gwamna Abba ya bai wa kowane dalibi kyautar Naira 50,000
Ga hotutnan yadda tarbar da kuma taron ya kasance: