
An tilasta wa Jakadan Isra’ila a Senegal barin harabar wata jami’a a Dakar sakamakon ihu da nuna kin jinin kashe-kashen da kasarsa take yi a Gaza.
Lamarin ya faru ne a Jami’ar Cheikh Anta Diop (UCAD), wacce ita ce mafi girma kuma mafi shahara a fannin ilimi a ƙasar a ranar Talata.
An gayyaci jakadan Isra’ila Yuval Waks ne don yin jawabi a wani taro kan dabarun hulɗar ƙasa da ƙasa amma da isarsa ɗalibai suka yi zanga-zanga kan zuwansa tare da rera taken goyon bayan Falasɗinu, kamar yadda wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta ya nuna.
“Daruruwan dalibai ne suka taru a wajen dakin taron, suna rera taken kalmar “’Yantar da Falasɗinu”, “’Yantar da Gaza” da kuma “Isra’ila mai aikata laifukan yaƙi”. In ji TRT.
Bidiyoyin da aka wallafa a intanet ya nuna dalibai suna ɗaga tutocin Falasɗinu tare da yin ihu ga jakadan da aka naɗa kwanan nan sun hana shi yin jawabin da aka shirya masa.
Jami’an tsaro sun raka Waks yayin da yake fita daga jami’ar, inda ya bar harabar ba tare da ya yi jawabin ga mahalarta ba. Masu zanga-zangar sun ci gaba da binsa suna rera taken da ɗaga tutoci har ya bar wajen.
Jakada Waks shine kuma jakadan Isra’ila da ke kula da ƙasashen Gambiya da Guinea da Guinea-Bissau da Cape Verde da Chadi, ya gabatar da takardun aikinsa ga Shugaban Senegal Bassirou Diomaye Faye a ranar 8 ga Mayu.