Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce, za ta soma hukunta mata ƴan kasuwa da ke yin shigar banza a Kafafan sada zumunta wato Social Media.
Babbar Kwamandar Hisbah ta mata Dr. Khadija Sagir Sulaiman ce ta bayyana hakan yayin tattauna wa da manema labarai.
Ta ce, tun bayan da Gwamnan Kano ya naɗa su a shugabancin Hisbah sun ziyarci da dama daga mata attajirai tare da yi musu nasiha da karrama wa.
Sai dai a yanzu wasu suna yin abubuwan da ba su dace ba, ta hanyar yin shigar banza a Social Media, abin da wasu mata ke koyi da su.
- Ganduje ya dakatar da shirin kafa wata Hisba a Kano
- Hisbah Ta Kama Matasa 5 Da Daura Aure Ba Bisa Ka’ida Ba
- Hisbah ta janye hannunta daga auren Mai Wushirya da Yar Guda
Ta ce, Hisbah ba za ta lamunci wannan ba domin ya saɓa wa addini.
Ta kuma yi kira ga mazajen ƴan kasuwa mata da su zamo masu kishi su sanya ido a kan matansu ba wai su barsu suna fitar da tsiraicinsu a Social Media ba.
Dr. Khadija ta ce, Hisbah na ci gaba da ƙarafafar mata wajen neman kuɗi domin halak ne a musulunci amma a yishi cikin mutunta ƙaʼidojin addini.
