Daga Nafiu Usman Rabiu
Gwamantin Kano za ta hade makarantun masu bukata ta musamman da sauran Makarantun jihar domin daliban su yi karatu tare.
Babban mataimaki na musamman ga gwamnan Kano a fannin ilimi, kuma tsohon kwamishinan ma’aikatar ilmi, Malam Tajuddeen Gambo, ya bayyan haka lokacin da yake zantawa da manema labarai.
Tajuddeen Gambo ya ce hade makarantaun wuri guda zai taimaka wajen samun kwarin gwiwar gudunar da karantunsu, sabanin yadda aka ware su daban.
“Yanzu an ci gaba a duniya ba’a ware masu bukata ta musamman da sauran Dalibai saboda haka muma zamu hade su wuri guda” inji shi.
Malam Tajuddeen Gambo ya kara da cewa a nan Kano akwai makarantun masu bukata ta musamman Tudun Maliki da Kuma ta Kofar Ruwa.