
Shugaban kamfanin Dangote Group, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana cewa har yanzu ana yiwa matatar man sa mummunar makarkashiya daga wasu manyan ’yan kasuwa da ke harkar man fetur.
Ana Kuma hakan ne da nufin dakile nasarar matatar da a yanzu, ta fi kowacce girma a nahiyar Afirka.
Dangote ya yi wannan zargin ne a yayin bikin cika shekara daya da matatar ta fara fitar da man fetur zuwa kasuwanni.
“Wasu manyan masu ruwa da tsaki a harkar mai na ƙasa da waje na kokarin ganin matatar da ta kai darajar dala biliyan 20 ba ta samu nasara ba.
“Tun daga watan Yunin 2025 zuwa yanzu, matatar ta fitar da lita biliyan 1 da miliyan 800 na man fetur zuwa kasuwannin waje, kuma tana da damar biyan bukatun cikin gida”. In ji shi.
Ya Kuma kara da cewa, tun daga lokacin da aka kammala aikin matatar a watan Satumbar 2024, Najeriya ta fara ganin karancin dogayen layukan neman fetur da suka dade suna addabar ’yan ƙasa fiye da shekaru 50.
Sannan Ya ce, sabbin motocin CNG 4,000 da ya shigo da su, za su samar da aƙalla ayyukan yi 24,000, ciki har da direbobi, makanikai da sauran ma’aikata.