Achraf Hakimi ya lashe ƙyautar gwarzon ɗan ƙwallon kafa na Afirka na 2025.
Matashi mai tsaron baya na Paris St Germain ya lashe ƙyautar ne a karon farko bayan shekara 52.
Hakimi dan asalin Morocco ya karɓi ƙyautar ne sakamakon nasarorin da ya samu a 2025 tare da Paris St Geramin ciki har da lashe Champions League da Ligue 1 da Coupe de France da kuma UEFA Super Cup.
Shi ne na farko daga Morocco da ya karbi ƙyautar tun bayan Mustapha Hadji a 1998, kuma mai tsaron baya na farko tun bayan ɗan kasar Zaire, Bwanga Tshimen a 1973.
Ɗan wasan Masar Mohamed Salah shi ne na biyu mai taka leda a Liverpool da kuma Victor Osimhen na Super Eagles mai wasa a Galatasaray a mataki na uku.
Kasar Morocco ce ta lashe yawancin ƙyautukan da aka raba daga ciki har da ta mace mafi ƙwazo a 2025 ga Ghizlane Chebbak mai taka leda a Saudiya da mai tsaron ragar Al-Hilal, Yassine Bounou a matakin mafi taka rawar gani a shekarar nan.
