Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir David Lawal, ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Ahmad Tinubu da gaza magance matsalolin tsaro da ke addabar ƙasar nan.
Babachir ya bayyana hakan ne a cikin shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels, inda ya ce gwamnatin Tinubu ba ta nuna ƙwarin gwiwar da ya dace wajen shawo kan matsalar tsaro da ta addabi al’umma.
Tsohon Sakataren gwamnatin Tarayya da ya yi aiki a karkashin marigayi Muhammadu Buhari, ya kuma jaddada cewa tsofaffin shugabannin ƙasa kamar Goodluck Jonathan da Buhari sun taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya a kasar nan.
