Gwamnatin Tarayya ta kuduri aniyar dakatar da shigo da Kifi daga kasashen ketare domin bunkasa kamun Kifin a cikin gida da kuma samar da wadataccen abinci a kasar da samar da ayyukan yi da kuma kara karfafa fitar da kayan amfani da basu da alakar man fetur zuwa kasashen ketare.
Ministan Bunkasa Tattalin Arzikin Teku, Adegboyega Oyetola ne ya sanar da hakan, a yayin wata ganawa da shugabanin kungiyoyin masu kamun Kifi a Abuja.
Ma’aikatar Ministan ce ta shirya ganawar, kan kokarin da gwamnatin tarayya ke ci gaba da yi, na saita fannin kamun Kifin a kasar.
Yace Dole ne kasar nan ta samar da wata sabuwar hanya, samar da Kifin da zai wadace ta.
Oyetola ya kara da cewa, gwamnatin tarayya ta himmatu kwarai da gaske wajen bai wa fannin goyon bayan da ya dace, musamman ta hanyar yin amfani da tsarin kimiyyar fasahar zamani da kuma zuba makudan kudade a fannin.
Kazalika, ya jaddada cewa; gwamnatin tarayya za ta kara kaimi wajen ganin ana samar da wadataccen Kifi a kasar, musamman domin rage dogaro a kan wadanda ake shigowa da su daga kasashen ketare, duba da cewa; fannin na bayar da gagarumar gudunmawa wajen kara bunkasa tattalin azikin kasar.
