Gwamnatin tarayya ta yaba da yadda Jami’ar Base ta samar da wani asibiti mai cike da kayan aiki na zamani da zai inganta harkokin kiwon Lafiya a kasar nan.
Ministan Lafiya da Dakta Muhammad Ali Pate, ya bayyana hakan lokacin da ya kai ziyara zuwa asibitin.
Dakta Pate, wanda uban Jami’ar Baze, Sanata Yusuf Datti Baba-Ahmed ya tarba, tare da manyan jami’an sa, ya zagaya wuraren kiwon lafiya da na koyar da likitanci na jami’ar.
A yayin ziyarar, Ministan ya nuna matuƙar gamsuwa da na’urorin zamani da asibitin ke da su, tare da tsarin haɗa koyarwa da bayar da ayyukan lafiya a wuri guda.
Ministan ya kuma yaba da yadda asibitin ya haɗa darussan koyarwa da horo na aikace-aikace a zahiri, wanda ke cike gibi tsakanin nazarin ilimi da aikin likitanci a aikace ga ɗalibai.
A jawabinsa, Baba-Ahmed, ya nuna godiya tare da sake jaddada aniyar jami’ar wajen ci gaba da kawo ingantaccen tsarin kiwon lafiya.
Asibitin Jami’ar Baze na bayar da nau’o’in ayyukan kiwon lafiya na musamman da suka haɗa da kula da cututtukan zuciya, kwakwalwa, da na cikin jiki.
