Gwamnatin tarayya bayyana karancin jini da rashin abinci mai gina jiki ga masu juna biyu a Nijeriya a matsayin babbar barazana ga lafiyar mata.
Wanann na fitowa ne ta bakin, Mataimakiyar Daraktar Sashen Abinci, ta ma’aiakatar lafiya ta tarayya Helen Achimugu, in da ta ce sakamakon Kididdigar Lafiya ta Kasa ta 2024, ya nuna cewa kashi 50 cikin 100 na mata masu juna biyu na fama da karancin jinni.
Ta ce kididdigar ta nuna Nijeriya ke kan gaba a Afirka kuma ta biyu a duniya wajen yawan yara masu karamin jiki.
- Gwamnatin Tarayya da bankin musulunci sun kafa makarantar koyar da harsuna a Kano
- Gwamnatin tarayya ta sha alwashin kammala aikin manyan hanyoyi a Katsina
A tattaunawar Wakiliyarmu Halima Ayyuba Adamu da likita a bangaren mata Dr. Nasir Abubakar na asibitin Muhammad Abdullahi Wase, yace matsala ce babba da ke kara yawa ga masu juna biyu kuma akwai dalilai dake janwo wa ake samun karancin jinnin.
Ya ce tun kafin watanni 3 na daukar ciki ya kamata ace mace tana shan maganin da zai taimaketa wajen samun karin jinni.
Dr. Nasir Abubakar yace muddin gwamnati ta taimaka wajen inganta tattalin arziki da kuma samar da mafita mai kyau ga masu juna biyu za’a samu raguwar matasalar.
