Gwamnatin Tarayya ta fitar da Naira biliyan 2 da miliyan 300 domin biyan bashin albashi da kuma kudaden ƙarin matsayi na malaman jami’oin mallakinta.
Ministan Ilimi Dakta Tunji Alausa ne ya bayyana hakan, inda ya ce matakin na daga cikin ƙoƙarin gwamnati na kawo ƙarshen takaddama da jayayya tsakaninta da ƙungiyoyin malaman jami’a.
“An biya kuɗin ne ta Ofishin Babban Akanta na Ƙasa, a matsayin rukuni na takwas na tsarin biyan bashin da malaman ke bin gwamnati tun wasu shekaru da suka wuce.
“Jami’o’in da abin ya shafa za su fara karɓar sakonnin biyan kuɗin daga yanzu zuwa kowane lokaci. In ji ministan.
