
Gwamnatin Tarayyar ta dakatar da aiwatar da sabon harajin Kwastam na kashi 4 cikin 100.
Hukumar ta fara karbar harajin ne kan kayayyakin da ake shigo da su cikin kasar.
Sanarwar hakan ya fito ne daga Ministan Kudi da Tattalin Arziki na kasa, Mista Wale Edun, ta bakin Babban Sakataren Ayyuka na Musamman a Ma’aikatar Kudi, Raymond Omachi a ranar Talata.
“Dakatarwar na zuwa ne bayan tattaunawa da masana harkokin kasuwanci da na tattalin arziki, da Kuma hukumomin gwamnati domin nazarin illar da harajin zai iya haifarwa ga tattalin arzikin kasa”.
“Mun fahimci cewa aiwatar da wannan haraji a wannan lokaci na iya haifar da koma baya ga harkokin kasuwanci, da haɓaka tsadar kayayyaki a kasuwa, wanda hakan zai ƙara wa talakawa nauyi,” in ji sanarwar.
‘Yan kasuwa da masu shigo da kaya sun bayyana damuwarsu game da karin harajin, wanda suka ce na iya dagula tsarin farashin kaya. A bayaninsa na dalilin janyewar.
A halin yanzu, dakatar da harajin zai ba gwamnati damar sake nazarin tsarin gaba daya, tare da hada kai da masu ruwa da tsaki domin samar da wata hanya ta dindindin da za ta inganta samun kudaden shiga.
Hukumar Kwastam ta Najeriya ta fara karbar harajin ne bisa tanadin dokar shekarar 2023, wanda ya tanadi karin kashi 4% a matsayin “processing fee” akan duka kayayyakin da ake shigo da su cikin kasa.