Gwamnatin sojin Jamhuriyar Nijar ta kafa majalisar tuntuɓa ta wucin-gadi, wadda aka fi sani da majalisar tuntuɓa ta Consultative Council of the Re-foundation ko kuma CCR a taƙaice.
Kafar yaɗa labarai da ActuNiger mai zaman kanta ta ruwaito cewa hukumomin ƙasar ne suka zaɓa tare da naɗa ƴanmajalisar, kuma an kafa ta ne bisa shawarar taron tuntuɓa da aka yi a ƙasar a watan Fabrairu.
A taron ne dai aka amince da tsawaita mulkin sojin da shekara biyar zuwa 10.
A majalisar akwai wakilai 194 da suke wakiltar ƙungiyoyi da dama, da matasa, da sarakuna, da mata, da jami’o’i, da mazauna ƙasashen waje, da sauransu,” kamar yadda rahoton ya bayyana.
Manufar majalisar ita ce ba wa gwamnatin shawara kan harkokin gwamnati da ciyar da ƙasar gaba, a gefe guda kuma suna tsare-tsaren tabbatar da dimokuraɗiyya.
Nijar da maƙwabtanta – Mali da Burkina Faso – duk suna ƙarƙashin mulkin soji ne, kuma alamu na nuna akwia sauran lokacin kafin komawarsu mulkin dimuraɗiyya.
