
Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta bayyana shirinta na saka takunkumi kan amfani da kafofin sada zumunta a ƙasar.
Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Intanet, Sidi Mohamed Raliou ne ya bayyana hakan yayin da yake bayani kan ayyukan ma’aikatarsa a gidan talabijin na ƙasar.
A cewarsa, suna nazarin hanyoyin da suka fi dacewa wajen ƙayyade amfani da kafofin sada zumunta, musamman ga masu amfani da su cikin jama’a da yawa, maimakon mutane ƙalilan.
“Nan ba da jimawa ba za a gabatar da shawara kan mafita tsayayya domin tabbatar da tsari mai tsafta wajen amfani da kafafen sada zumunta a Nijar,” in ji Minista Raliou.