
ukumar Kula da Shige da Fice ta kasar nan (NIS) ta fara korar bakin haure 192 da aka same su da laifin damfara ta yanar gizo a kasar.
Alfijir labarai ta rawaito cewa rukuni na farko na bakin hauren guda 42 an kore su ne ranar Lahadi, yayin da wani rukuni zai tashi ta jirgin sama zuwa kasashensu daban-daban ranar Litinin da Talata.
A watan Disamba 2024, Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Najeriya (EFCC) ta cafke mutane 792 daga wata kungiya da ake zargi da damfarar cryptocurrency da kwaikwayon soyayya.
An cafke wadanda ake zargi a wani gini mai hawa bakwai a Victoria Island, dake Lagos. An ce bakin hauren suna amfani da ginin don “koyar da ‘yan Najeriya yadda ake shirya damfaran zuba jari.
Daga cikin ‘yan kungiyar akwai ‘yan kasar Sin 114, ‘yan Philippines 40, biyu kuma ‘yan Khazartan, daya daga Pakistan, da daya daga Indonesia.
Hukumar yaki da rashawa ta bayyana wannan aiki a matsayin “cikakken kamawa mafi girma na damfaran yanar gizo a kasar a rana guda.”
EFCC ta gurfanar da wadanda ake zargin a kotun tarayya dake Lagos.
Kotu ta kuma umurci kwantirola janar ta Hukumar Kula da Shige da Fice ta Najeriya (NIS) da ya mayar da bakin hauren kasarsu cikin kwanaki bakwai bayan sun kammala zaman kurkuku.
