
Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano Ali Haruna Makoda ne ya bayyana hakan a ranar Laraba, yayin bikin raba takardun shaidar ƙammala karatu ga ɗaliban babbar makarantar sakandare ta Maryam Aloma.
Wannan mataki na daga cikin shirye-shiryen gwamnati na inganta fannin ilimi da kuma shawo kan ƙarancin malamai masu ƙwarewa da ake fuskanta a makarantun sakandaren jihar.
“Daukar sabbin malamai musamman a bangaren lissafi ya zama wajibi, duba da muhimmancin da darasin ke da shi wajen ƙarfafa tunani da ƙwarewar ɗalibai a fannoni da dama”. In ji shi.
Kwamishinan ya kuma ce, matakin na daga cikin hanyoyin da gwamnatin jihar ke bi domin tabbatar da dorewar nasarorin da aka cimma a shekarar ilimi ta 2025.