
Gwamnatin Kano ta ware dalibai 55 da ta zabo daga kananan Hukumomi 44 domin kai su Masira domin su karanci shari’ar Musulunci.
Darektan Sashin Ilimin Larabci Da Karatun Addinin Musulunci Na Ma’aikatar Ilimi Ta Kano, Safiyanu Abubakar ne ya bayyana haka a yayin taron kara wa juna sani na kwanaki biyu da aka shiryawa malaman makarantun sakandare sashen harshen Larabci da karatun addinin musulunci.
A jawabinsa Darakta ya ce, gwamnatin ta shirya taron ne dan farfado da sashin karatun addinin musulunci da harshen larabci don ganin ilimi ya fadada a jihar.
Safiyanu ya kuma kara da cewa, saboda haka suka yiwa dalibai daga kanannan hukumomi 44 jarabawa domin kai su Masar su karanto shariar musulunci.