
Ma’aikatar Muhalli da Sauyin Yanayi ta Jihar Kano za ta gyara dukan motocin kwashe shara da na sauran ayyuka da ke ƙarƙashin Hukumar (REMASAB) da suka lalace, kafin ƙarshen shekarar 2025.
Kwamishinan ma’aikatar, Dakta Dahir Muhammad Hashim ne ya bayyana hakan a lokacin wata ziyara ta musamman da ya kai ofishin REMASAB domin duba halin da motocin aikin ke ciki a ranar Litinin.
“Matakin gyaran motocin zai kasance karo na biyu cikin shirin gyare-gyaren da gwamnati ke gudanarwa, domin dawo da dukkan motocin aiki cikin sahun aiki yadda ya kamata”. In ji shi
Kwamishinan ya kuma ce, ƙuduri na nuna jajircewar gwamnatin Kano a ƙarƙashin Gwamna Abba Kabir Yusuf wajen inganta tsabtar muhalli da kare lafiyar jama’a, tare da tabbatar da cewa hukumar REMASAB na da dukkan kayan aikin da suka dace domin gudanar da aikinta cikin nagarta.