Gwamnatin Kano ta ce za ta ɗauki nauyin karatun dukkan mutanen da suka musulunta a faɗin jihar, domin ba su damar samun ingantaccen ilimin addinin Musulunci ba tare da fuskantar matsalar biyan kuɗin makaranta ba.
Shugaban kwalejin koyon Shari’a da Ilimin Addinin Musulunci ta LEGAL, Dr Tamasi Ali Ma’az, ne ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da manema labarai.
Dr Tamasi ya ce matakin wani ɓangare ne na ƙoƙarin gwamnatin Kano na tallafa wa sabbin musulunta wajen samun ilimin addinin, domin su fahimci koyarwar addinin tare da sauƙaƙa musu gudanar da rayuwarsu bisa ƙa’idojin Musulunci.
DrrTamasi Ali Ma’az ya ce ɗaukar nauyin karatun zai ragewa sabbin musuluntar nauyin kuɗaɗen makaranta, musamman ganin wasu daga cikinsu na iya fuskantar ƙalubalen samun kuɗin karatu da samun ilimin addinin na musulunci.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Dr Tamasi na cewa shirin zai baiwa sabbin tuban damar samun ilimi cikin sauƙi, tare da ƙarfafa musu gwiwa wajen ci gaba da karatunsu da kuma fahimtar addinin Musulunci yadda ya kamata.
