 
        Gwamnatin Jihar Kano tayi watsi da rahoton da Cibiyar Wale Soyinka ta fitar, wanda ya zargi jihar da keta ‘yancin faɗin albarkacin baki na ‘yan Jarida
A wani taron manema labarai da Kwamishinan yaɗa labarai da al’amuran cikin gida Kwamared Ibrahim Abdullahi Wayya ya kira ya bayyana rahoton a matsayin mara tushe balle makama da tushe ko hujja, domin gwamnatin Kano tana mutunta ‘yancin yan Jarida na bayyana ra’ayoyinsu bisa doka da tsarin mulki.
Ya ce gwamnatin jihar tana maraba da duk wata sukar da aka gina bisa gaskiya da hujjoji, amma ba zata lamunci yadda aka kirkiri karya domin bata sunan gwamnati ba.
Gwamnatin Kano za ta cigaba da kyautatawa ‘yan jarida
Ƴan sanda sun tsare ɗan jaridar bayan DG Protocol ya shigar da korafi a kansa
Kisan ‘yar jarida a Katampe ya tayar da ‘yansanda tsaye a Abuja
Kwamishinan ya kuma bayyana cewa gwamnatin Abba Kabir Yusuf tana ci gaba da tabbatar da mulkin dimokuraɗiyya da kare ‘yancin yan Jarida ta hanyar bude kafafen sadarwa da haɗin kai da kungiyoyin farar hula.
Idan za’a iya tunawa a cikin rahoton na Cibiyar Wale Sonyinka mai taken “Shrinking Freedoms: 2024 Journalism and Civic Space Status Report”, Cibiyar ta bayyana cewa Jihar Kano ta kasance daga cikin jihohi guda uku da ke kan gaba wajen samun rahotannin keta ‘yancin faɗin albarkacin baki na yan jarida, Inda a cikin rahoton bayan Kano aka sanya Lagos da Abuja.
Sai dai, kwamishinan ya a fito yace wannan Rahoton bashi da madogara kuma an fitar da shi da wata manufa sannan Cibiyar bata da Wakilai a jihohin Najeriya kan abinda ke faruwa musamman jihar Kano.
Kwamishinan na yada labarai Kwamared Ibrahim Wayya yace gwamna Yusuf ya samu lambobin yabo masu yawa daga jaridun kasar nan saboda kyakkyawar fahimtar da ke tsakaninsa da manema labarai da suka hada da Jaridar Leadership wacce ta bashi gwamnan da yafi sauran gwamnonin Najeriya a bangaren ciyar da Ilimi gaba.
Sannan ya samu lambar yabo ta “African Governor of the Year for Good Governance” daga African Leadership Magazine da sauransu.
Kwamishinan yace Kano na cikin jerin jihohin Najeriya da suke mutunta aikin Jarida Wanda shi ne yasa manyan Jaridun Najeriya suka karrama gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf.
Kwamishina Wayya ya bada misali da zanga zangar yaki da rashin kyakkyawar gwannati a Najeriya,a shekarar 2024 Inda yace gwamna Yusuf ne kadai a duk Najeriya da ya karbi masu zanga zangar da kyakkyawar niya .
Ya ce kuma gwamnatin Kano ta na ayyukanta a bude kuma haka zata cigaba da yi.

 
           
           
           
           
         
         
         
         
         
         
           
           
          