Gwamnatin Kano ta ce a shekarar da ta gabata ta samu nasarar gano masu dauke da cutar kuturta 319, tare da warkar da su ba tare da rasa rai ba, hadi da shan alwashin ci gaba da yaƙi da cutukan da ake iya rigakafinsu, da nufin kare lafiyar al’ummar Kano musamman mata da kananan yara.
Kwamishinan Lafiya na Kano Dr Abubakar Labaran Yusif ne ya bayyana hakan yayin wani taron bikin tunawa da ranakun cutukan da aka daina kulawa da su, da ranar cutar kuturta, da kuma ranar cutar daji na duniya.
Kwamishinan ya ce cutukan da aka daina kulawa da su irin su dundumi, Tundurmi, kumburin ƙafa, da tsargiya, na ci gaba da shafar rayuwar al’ummar Kano, inda yace daga watan janairun 2025 zuwa Satumbar ta,
cibiyar kula da cutar daji ta kano ta samu masu dauke da cutar 444, inda cutar dajin mahaifa da ta Mama suka fi yawa, lamarin da ke nuna muhimmancin rigakafi, yin gwaji da wuri da kuma magani cikin lokaci.
- Gwamnatin Kano Ta Musanta Rahoton Haihuwar Jarirai 700,000
- Gwamnatin Kano ta kaddamar da feshin maganin sauro a wasu unguwanni
Kwamishinan ya kuma ƙaddamar da zagaye na biyu na shirin rigakafin cutukan da suke saurin hallaka kananan yara ‘yan kasa da shekaru 5 mai taken SARMAAN II zagaye na biyu, inda malaman lafiya zasu bi gida-gida tare da baiwa yara masu watanni 1 zuwa shekaru 5 a duniya maganin Azitromaisin domin kare su daga kamuwa da matsalolin limoniya, gudawa da cutukan dake saurin kashe yaran.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Dr Labaran na jan hankalin al’umma da su dinga saurin zuwa a duba lafiyar su a duk lokacin da suka ji sauyi a jikin su.
