
Gwamnatin jihar Kano ta sanar da fitar da sama da Naira miliyan 150 domin sake gina masallacin Gadan da ke karamar hukumar Gezawa, wanda wani matashi ya kone masallata 23
Kwamishinan Yada Labarai Da Alamuran Cikin Gida Na Jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ne ya bayyana cewa gwamnati hakan cika alkawarin da gwamnan jihar, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya dauka ne yayin ziyarar jaje da ya kai wa al’ummar yankin a lokacin da lamarin ya faru a 2024.
A cikin ayyukan da gwamnati za ta aiwatar ga al’ummar kauyen har da gina makarantar Islamiyya da samar da sabbin ofisoshi da gyara bandakuna da kuma samar da wutar lantarki ta hasken rana tare da fanfofan tuka-tuka, domin inganta rayuwar al’ummar yankin baki daya.
Gwamnan ya bukaci mutanen Gadan da su bayar da hadin kai wajen tabbatar da nasarar aikin, tare da kula da sabon ginin bayan kammalawa.
Wannan shiri na daya daga cikin kokarin gwamnatin jihar Kano na inganta wuraren ibada da kuma inganta ababen more rayuwa ga al’ummar jihar.