Tsohon kwamishinan ilimi na jihar Kano, Muhammad Sanusi S. Kiru, ya zargi gwamnatin Kano da sayar da filayen makarantar sakandaren Maikwatashi da aka rusa.
Kwamishinan ya yi zargin cewa, kowanne fili da aka yanka ana sayar da shi akan Naira miliyan 100.
A wata wasika da ya aika wa Gwamna Abba Kabir Yusuf, tsohon kwamishinan ya bayyana rashin jin daɗinsa kan yadda aka rusa makarantar tare da ɗauke ɗalibai zuwa Kaura Goje ba tare da an kammala sabon gini ba, lamarin da ya ce ya jefa ɗalibai da malamai cikin halin wahala.
“A lokacin da nake kwamishina, na taɓa yin sauyin makarantu irin wannan, amma sai da aka kammala ginin sabuwar makaranta kafin a mayar da ɗalibai, domin kauce wa tsaiko a harkar karatu.
“A maimakon a sayar da filin makarantar, kamata ya yi gwamnati ta maida wurin wajen ayyukan ci gaban al’umma, kamar filin motsa jiki ko cibiyar ci gaban al’umma. In ji shi.
A baya gwamnatin ta bayyana dauke makarantar ne a bisa dalilin nisa da jama’a da kuma jefa daliban cikin hadari kan hanyarsu na zuwa makarantar.
Tuni wasu mazauna wuraren suka nuna farin cikinsu dangane matsar da makarantar.
