
Aminu Abdullahi Ibrahim
Gwamnatin Kano ta kaddamar da koyar da sana’o’in dogaro da kai a garin Getso da ke karamar hukumar Gwarzo.
An kaddamar da bayar da horon ne a cibiyar koyar da sana’o’i dake Getso a Talatar nan.
Wannan na zuwa ne bayan da gwamnatin Kano ta gyara cibiyar tare da sake bude ta.
Da yake jawabi shugaban cibiyar kuma shugaban jam’iyar NNPP na karamar hukumar Gwarzo, Abdulkadir Ahmad Getso, ya ce an debi kashin farko na mutane fiye da 200 da suka hada da maza da mata.
Ya ce za a koyar da su sana’o’i daban daban ciki har da dinki na zamani.
Abdulkadir Getso, ya ce za a dauki sati 8 ana koyar da su bayan an kammala kuma za a sake daukar wasu sabbin daliban.
A nasa bangaren mai magana da yawun gwamnan Kano Sunusi Bature Dawakin Tofa, wanda ya jagoranci wakilan cibiyar yada labarai da hulda da jama’a (NIPR) domin sheda kaddamar da bayar da horon da wasu aiyukan gwamnatin Kano, ya bukaci wadanda zasu amfana da su mayar da hankali wajen koyan sana’o’in.
Ya kuma yi kira a gare su da su zama jakadu nagari tare da dogaro da kansu.
Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya kara da cewa gwamnatin Kano karkashin Abba Kabir Yusuf, ta himmatu wajen hidimtawa al’umma da bunkasa cigaban matasa.