Aminu Abdullahi Ibrahim
Gwamnatin Kano ta raba kayayyakin aiki na kariya ga ma’aikatan a kananan hukumomin Kano 44.
Darakta Janar na hukumar dakile yaduwar cututtuka ta jihar Kano (KNCDC) Farfesa Muhammad Adamu Abbas, ne ya bayyana haka a Larabar nan yayin raba kayayyakin a ofishin hukumar.
Ya ce abubuwan da za a raba sun hada da kayayyakin kariya ga marasa lafiya da ma’aikata.
Ya kara da cewa kayan sun hada da Gilashin Ido da Robar Ido da Rigar kariya da Safar Hannu da kuma takunkumin rufe hanci don kare kamuwa daga cututtuka masu yaduwa.
Farfesa Abbas ya kuma ce zasu kai magunguna asibitoci domin kula da marasa lafiya.
Ya ce hikimar bayar da kayan shine domin kowane asibitoci dake wajen gari ya samu kayan aiki don bayar da taimakon gaggawa kafin zuwa cikin gari.
Ya godewa shugabanin kananan hukumomi da sarakunan garggajiya bisa hadin kan da suke baiwa hukumar ta KNCDC a koda yaushe.
