Gwamnatin Jihar Kano ta musanta wani rahoto da jaridar Daily Trust ta wallafa, wanda ya yi ikirarin cewa ana sa ran haihuwar jarirai har 700,000 a jihar a shekarar 2026.
Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Jami’ar Hulɗa da Jama’a ta Hukumar Kula da Asibitocin Jihar Kano, Samira Suleiman, ta fitar a ranar Litinin, 26 ga watan Janairu, 2026.
A cewar sanarwar, rahoton ya jingina bayanin ga Shugaban Hukumar, Dr. Mansur Mudi Nagoda, duk da cewa bai halarci taron yaye ɗalibai na Kwalejin Kiwon Lafiya da Fasaha ta Sardauna da ke Kano ba, inda aka ce a can ne ya faɗi hakan.
Sanarwar ta jaddada cewa Dr. Nagoda bai taɓa faɗin irin wannan magana ba, ko a wajen taron ko a wani waje daban.
Gwamnatin jihar ta bayyana rahoton a matsayin kuskure mai tsanani a aikin jarida, tare da neman jaridar Daily Trust ta janye rahoton a bainar jama’a.
