
Gwamnatin Kano ta bankando Naira Miliayan 28 na ma’aikata da aka wawure.
Kudaden da ka gano na ma’aikatan kananun hukumomin jihar ne da suka yi ritaya ko kuma suka mutu amma aka ji gaba da biyansu.
Bayanin gano kudin na kunshe ne a cikin wata sanarwar da ofishin sakataren Gwamnatin Kano ya fitar a ranar Asabar.
“A iya watan Maris an gano cewa an yi badaƙalar albashin ma’aikatan ƙananun hukumomi da takai kusan ta naira miliyan 27,824,395.40.
“Albashin na ma’aikata 247 ne da ake kyautata zaton sun yi ritaya ko kuma sun mutu amma har yanzu ba’a dania fitar da hakokin na su ba daga asusun gwamnati ba.” in ji sanarwar.
Sanarwar ta ce, tuni aka bibiyi yadda ake fitar da kuɗaɗen sannan aka mayar da su cikin asusun ma’aikatar Kananun Hukumomin jihar.
Gwamnati ta kuma tabbatar da cewa, za’a binciko dukkanin masu hannu a wannan badakala da kuma hukunta su.