Gwamna Abba Kabir Yusuf yana jawabi a yayin taron
Gwamnatin Kano ta haramta kafa kowace ƙungiya ta Hisba mai zaman kanta a Jihar #hisba.
Ta kuma ba da umarnin jami’an tsaro da su kama tare da gurfanar da duk wanda aka samu yana kokarin kafawa ko shiga kungiyar.
Kwamshinan yada Labarai Kwamared Ibrahim Abdullahi Wayya ne ya bayyana hakan taron manema labarai a ranar Juma’a.
“Kamar yadda dokar kafa hukumar Hisba da aka yiwa gyara a shekarar 2005 ta nuna, haramun ne a kafa hukumomin Hisba guda biyu a jihar.
“Kafa hukumar Hisba mai zaman kan ta wadda aka yiwa lakabi da Fisabillalahi da tsohon gwaman Kano Dr. Abdullahi Ganduje zai kafa ya saba dokar kasa
“Don haka duk wani yunmurin kirkirar sabuwar Hisba mai zaman kanta karya doka ne kuma barazana ce ga zaman lafiya da tsaron jihar Kano.” In ji Kwamishinan
Wayya ya kuma gargadadi al’umma da su guji shiga kungiyoyin da basu da sahalewar gwamnati.
Ya kuma tabbatar wa jama’a cewa za ta ci gaba da daukar matakan da suka dace domin tabbatar da zaman lafiya da bin doka a fadin jihar.
