
Gwamnatin jihar Kaduna tace zata dawo da aikin tsaftace muhalli na karshen wata.
A cewar gwamnatin hakan ya biyo bayan yadda al’ummar jihar ke sakaci wajen tsaftace muhallansu wanda ke haddasa iftila’i daban daban, ciki har da ambaliyar ruwa da cutuka.
A zantawarsa da manema labarai, kwamishinan muhalli na jihar Kaduna Abubakar Buba, yace gwamna Uba Sani ya bada umarnin dawo da tsaftar muhalli daga ranar Asabar din karshen watan Oktoba mai kamawa.
Kwamishinan yace tuni suka fara tattaunawa da dukkan masu ruwa da tsaki da suka hada da jami’an tsaro, da masu sarautun gargajiya, da shugabannin kananan hukumomi domin wayar da kan al’umma akan muhimmancin tsaftar muhalli.
Abubakar Buba yace zasu bullo da wani tsari na karrama duk unguwar da tafi kowace tsafta a kowane wata tare da bada kyautuka.
Yace daga cikin kyautukan akwai bishiyu wadanda za a dasa domin kiyaye sauyin yanayi.