Gwamnan jihar Sakkwato Ahmad Aliyu, ya ce gwamnatinsa za ta gudanar da bincike kan kisan farar hula da sojojin sama suka yi.
Gwamnan ya furta hakan ne yayin da yake jajanta wa al’ummar jihar kan lamarin kisan jiragen saman sojojin suka yi a yayin da suka kai hari kan ‘yan ta’addan Lakurawa a ƙauyukan Gidan Bisa da Runtuwa da ke yankin ƙaramar hukumar Silame a daren Litinin.
Rahotanni sun ce an tafka kuskuren ne yayin da dakarun ke ƙoƙarin fatattakar Lakurawa ‘yan ta’adda a jihar.
Rundunar sojojin haɗin gwiwa ta ‘Operation Fansan Yamma’, ta buƙaci jama’a da su riƙa dogara da ingantattun bayanai domin hana yaɗa rahotannin ƙarya
Wata sanarwar da Kakaki rundunar, Laftanar Kanal Abubakar Abdullahi ya fita a matsayin maratani ga lamarin ya ce, harin da jiragen suka na bisa tsari kuma a kan ‘yan taddar ne ba farar hula ba.
“Rahotannin da ke cewa wani jirgin yaƙin sojojin ne ya kai harin bam kan wasu kauyuka a ƙaramar hukumar Silame, rundunar ta tabbatar da cewa inda ta kai harin na da alaƙa da ƙungiyar ƴan ta’adda ta Lakurawa. In ji sanarwar.