Gwamnatin Tarayya ta ƙara Asibitin Koyarwa na Aminu Kano cikin jerin cibiyoyin lafiya da za su rika yi wa marasa lafiya wankin ƙoda a rage kuɗi daga Naira 50,000 zuwa Naira 12,000 a kowane zama.
A baya, sanarwar farko da gwamnati ta fitar ta nuna babu asibitoci daga Yankin Arewa maso Yamma da za su amfana da wannan tallafi, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin al’umma.
Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin sadarwa da tsare-tsare, Daniel Bwala, ya ce asibitocin farko sun haɗa da na Lagos, Abuja, Ibadan, Owerri da Maiduguri, kuma za a ƙara wasu kafin ƙarshen shekara.
Sai dai a cikin sabuwar sanarwar da Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya ta fitar a ranar Laraba, ta tabbatar da cewa Asibitin Koyarwa na Aminu Kano ya shiga cikin shirin.
Ma’aikatar ta kuma jaddada cewa za a ci gaba da ƙara wasu asibitoci a sassa daban-daban na ƙasar, tare da tabbatar da cewa ba a manta da kowana yanki ba.
