
Kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah reshen jihar Kaduna ta bukaci gwamnatin jihar ta gaggauta biyan diyya ga iyalan Fulani da suka rasa ‘yan uwansu a harin da aka kai musu a kauyen Tanda, da ke Karamar Hukumar Jema’a dake Kudancin Jihar Kaduna.
Shugaban kungiyar, Abdulhamid Musa Albarka, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce, harin da aka kai ranar 28 ga Watan Satumba ya nuna yadda manoman yankin ke cin karensu ba babbaka akan Fulani makiyaya.
“Harin ya yi sanadiyyar rasuwar Suleiman Idris, yayin da wasu makiyaya 6 suka samu munanan raunuka, bayan da wasu manoma suka kai musu farmaki.” In ji shi
Shugaban kungiyar ya kuma bukaci gwamnatin jihar Kaduna da karamar hukumar Juma’a da su tallafawa iyalan wadanda harin ya shafa domin hakkinsu a matsayinsu na ‘yan kasa.
Rikicin manoma da makiyaya ya daɗe yana faruwa a sassa daban-daban na Najeriya inda Mafi yawan lokuta rikicin na samo asali bisa zargin barin dabbobi su shiga gonakin manoma su yi musu ɓarna.