
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sanya hannu a kan ƙwarya-ƙwaryan kasafin kuɗin shekara ta 2025, bayan da majalisar dokokin jihar ta amince da shi tare da yin gyare-gyare daidai da bukatun al’umma.
Taron sanya hannu kan kasafin ya gudana ne a fadar gwamnatin jihar dake Kano, inda gwamnan ya jaddada cewa kasafin na bana zai fi karkata ne zuwa manyan ayyukan raya kasa da walwalar jama’a.
A jawabinsa, Gwamna Abba ya bayyana cewa kasafin ya fi karkata ne wajen manyan ayyukan raya jiha, inganta harkar ilimi da lafiya, samar da ayyukan yi ga matasa da kuma habaka ababen more rayuwa.
Ya bukaci dukkan ma’aikatu da hukumomin gwamnati da su himmatu wajen aiwatar da kasafin yadda ya kamata, domin tabbatar da manufofin gwamnatin Kano sun cimma burinsu.
Shugaban majalisar dokokin jihar Kano, Alhaji Jibrin Isma’il Falgore, ya bayyana cewa majalisar ta gudanar da cikakken nazari da gyare-gyare kafin ta amince da kasafin, domin tabbatar da cewa ya dace da bukatu da muradun al’ummar jihar.