Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sake nada kwamishinoni 2 da ya sauke a kwanakin baya, a wasu mukamai tare da nada masu ba shi shawara.
Bayanin hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar.
Wadanda aka nada sun hada da Ahmad Muhammad Speaker a matsayin mai bawa gwamna shawara na Musamman kan Yada Labarai, sai Injiniya Ahmad a matsayin mai bawa gwamna shawara kan ayyuka , da kuma Sani Abdullahi Tofa a matsayin Mai bawa gwamna Shawara kan ayyuka na Musamman.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da naɗin tsohon kwamishinan kudi Ibrahim Jibrin Fagge a matsayin Shugaban Hukumar Kula da Ayyukan Kananan Hukumomi, da Hajiya Ladidi Ibrahim Garko a matsayin Shugabar Hukumar kula da ma’aikatan gwamnatin Jihar Kano.
Sanarwar ta ce nade naden sun fara aiki nan take.