Aminu Abdullahi Ibrahim
Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya jajantawa Al’ummar Jigawa da iyalan Gwamnan jihar bisa rasuwar mahaifiyar sa Hajiya Maryam da Dansa Abdulwahab.
Abba Kabir Yusuf yayi wannan jaje ne yayin ta’aziyar da ya kaiwa gwamnan Jigawa ranar Lahadi a gidan sa dake Kafin Hausa.
Gwamnan ya bayyana mutuwar su amatsayin babban rashi ga al’ummar musulmi.
Abba Kabir Yusuf, ya kuma yi addu’ar Allah yajikansu ya baiwa iyalansu hakurin jure rashi.
Wakilin mu Aminu Abdullahi Ibrahim ya ruwaito cewa da yake nasa jawabin Gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi Dan Modi, ya godewa gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf bisa nuna soyayya da kauna ga Iyalansa.
Umar Namadi, ya ce ba zai manta da irin yadda Gwamnan Kano ya nuna damuwa kan rashin Mahaifiyar sa da Dansa ba.
Idan za a iya tunawa a ranar Laraba ne mahaifiyar gwamnan Jigawa Hajiya Maryam ta rasu kwana daya bayan rasuwar ta ne Dan sa Abdulwahab shi ma ya rasu a hatsarin mota.