
Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusif, ya jinjinawa Kungiyoyin Fararen Hula tare da bayyana su a matsayin garkuwa ga talakawan Najeriya.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Talata, a yayin kaddamar da babban taron kungiyoyin fararen hula na farko a tarihin jihar, wanda Ma’aikatar Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida ta jihar ta shirya.
Mataimakin Gwamna, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ne wakilce shi.
“Wadannan kungiyoyi na taka muhimmiyar rawa wajen saukaka rayuwar al’umma da kuma samar da mafita ga matsalolin da ke fuskantar jama’a a matakin kasa da Kuma kananan hukumomi”. In ji shi.
Gwamna Yusif ya Kuma ce, gwamnatinsa a shirye ta ke wajen karfafawa guiwar Kungiyoyin Fararen Hular da ke fadin Jihar, domin su ci-gaba da gudanar da ayyukansu na inganta rayuwar al’umma da kuma nema musu maganin matsalolin su.
Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, a jawabinsa, ya bayyana taron a matsayin wata muhimmiyar dama ta hada kai da fadada fahimta tsakanin gwamnati da kungiyoyin fararen hula a jihar.
Ya kuma yi nuni da cewa wadannan kungiyoyi na da matukar muhimmanci wajen gina demokaradiyya da inganta shugabanci nagari.
A yayin taron, Mai Martaba Sarkin Kano na 16, Malam Muhammadu Sanusi II, ta bakin wakilinsa, Hakimin Rimin Gado, Alhaji Auwalu Idi Yakasai Kuma Dan Malikin Kano, ya bayyana Kungiyoyin Fararen Hula a matsayin jiga-jigan da ke taka rawa a fagen sadaukar da kai wajen tallafa wa al’umma.