
Daga Aminu Abdullahi Ibrahim
Gwamnan Kano ya ja hankali matasa masu kwacen Waya da su dena.
Gwamnan yayi wannan Jan hankali ne yayin da yake jawabi bayan dawowar sa Kano daga kasar Saudiyya ranar Laraba.
Ya ce gwamnati ba zata zuba ido tana ganin wasu na aikata ta’adar kwacen Waya ba.
Abba Kabir Yusuf, ya ce sun san wadanda suke zuga matasan kuma suke saka su kwacen Waya.
Ya ce zasu dauki mataki akan masu daukar nawin masu kwacen Waya a jihar Kano.
Ya jajantawa ‘yan wasan jihar Kano 22 da suka rasu sakamakon hatsarin mota.
Abba Kabir Yusuf, ya kuma jajantawa ‘yan kasuwar fam santa da ifti’la’in gobara ya shafa.
Ya ce gwamnati zata tallafa su da bijiro da aiyukan cigaba a kasuwar.