Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya zargi Gwamnatin Tarayya da amfani da Hukumar EFCC domin tsangwama da gallaza masa da wasu jami’an gwamnatinsa, bisa dalilin ƙin amincewarsa da sauya sheƙa zuwa Jam’iyyar APC mai mulki.
Gwamnan ya bayyana cewa tun bayan da ya fito fili ya nuna matsayinsa na ci gaba da kasancewa a jam’iyyar adawa, ana ƙara matsa masa lamba ta hanyoyi daban-daban.
Ya ce wannan matsin lamba ya haɗa da bincike da kuma kiran wasu jami’an gwamnatinsa zuwa EFCC, matakin da ya bayyana a matsayin siyasa da aka sanya mata rigar yaƙi da rashawa.
Bala Mohammed ya ce irin wannan salon yana nuna ƙyamar adawa tare da amfani da siyasar tsoratarwa, yana mai jaddada cewa ba zai bari barazana ko tsangwama su karkatar da shi daga abin da ya yi imani da shi ba.
Ya kuma yi kira ga al’umma da hukumomin ƙasa da su sanya ido kan yadda ake amfani da hukumomin gwamnati wajen murkushe ‘yan adawa, yana mai cewa dimokuraɗiyya ba ta bunƙasa ta hanyar tsoro, illa ta adalci da girmama ra’ayin juna.
