Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya kare matakin da jam’iyyar PDP ta dauka na mika tikitin takarar shugaban kasa a 2027 zuwa yankin Kudu, yana mai cewa matakin na da nufin samar da fahimta da hadin kai a cikin jam’iyyar.
Kwamitin zartarwa na jam’iyyar na kasa ne ya cimma wannan matsaya ne a farkon makon nan, yayin taron kwamitin a Abuja, inda ta kuma tabbatar da Iliya Damagum a matsayin babban shugabanta na kasa.
A wata hira da yayi da tashar AIT bayan jamiyyar ta yanke hukuncin, Bala Mohammed wanda shi ne shugaban kungiyar gwamnonin PDP a Najeriya ya bayyana hakan a matsayin dabarar da za ta hada kan jamiyyar daga dukkanin sassan kasar, wanda hakan zai taimaka wajen kawo karshen jamiyya mai mulkin kasa wato APC a zaben 2027.
Gwamnan Bauchi ya bukaci ‘yan Najeriya da su rika ganin siyasa ta wuce son rai, yana mai jaddada sadaukarwa da kuma muradin jam’iyyar tasu baki daya.
