Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sanya hannu kan dokar kafa Hukumar Kula Da Cutuka Masu yaduwa da dokar kafa Hukumar Jami’an Tsaro ta jiha.
Gwamnan ya yi hakan ne a wani zama na Majalisar Zartaswa ta jihar a ranar Talata.
Haka kuma, gwamnan ya amince da gyaran dokar Hukumar Kula Da Sufuri ta jihar Kano, wanda zai inganta harkokin sufuri a jihar.
Sa hannu a dokokin ya biyo bayan amincewa da kudurorin kafa sabbin hukumomin ne da Majalisar Dokokin jihar ta yi. Ga yadda bikin sa hannun ya kasance a cikin hotuna.
