
Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya naɗa kyaftin ɗin Super Eagles, Ahmed Musa a matsayin sabon shugaban gudanarwar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars.
Cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan jihar, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ya ce, naɗin wani ɓangare ne ƙoƙarin ƙarfafa ƙungiyar gabanin fara sabuwar kakar gasar Firimiya ta kasar.
Dawakin Tofa ya ce, an naɗa Ahmed Musa wanda ɗan wasan ƙungiyar ne bayan tuntuɓar masu ruwa da tsaki a harkokin wasanni a faɗin jihar.
A watan Octoban 2024 ne Kano Pillars ta sanar da ɗaukar kyaftin ɗin na Najeriya, Ahmed Musa domin buga mata wasanni Premier Najeriya.

Sabbin Hukumar Gudanarwa
Gwamnan ya kuma nada sabbin ‘yan hukumar gudanarwa karkashin jagorancin Ali Mohammed Umar Nayara, sauran wadanda aka nada a matsayin jami’an gudanarwar kungiyar sun hada da Rilawanu Idris Malikawar Garu da Abubakar Dandago da Aminu Malesh.

Sauran sune:
- Ali Muhammad Umar (Nayara) –
- Salisu Mohammed Kosawa
- Yusuf Danladi Andy Cole
- Idris Malikawa Garu
- Nasiru Bello
- Muhammad Ibrahim (Hassan West)
- Abdulkarim Audi Chara – Member
- Muhammad Danjuma Gwarzo
- Mustapha Usman Darma
- Umar Dankura
- Ahmad Musbahu
- Gambo Salisu Shuaibu Kura
- Rabiu Abdullahi
- Aminu Ma’alesh
- Safiyanu Abdu
- Abubakar Isah Dandago Yamalash
- Ismail Abba Tangalash