
Daga Aminu Abdullahi Ibrahim
Gwamnan ya sanar da hakan ne yayin liyafar buda baki ga daliban 53 Jim kadan da isowarsu Kano a ranar Juma’a da dare.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce, gwamnati za ta ba wa daliban takardunsu na daukar aiki ba tare da bata lokaci ba.

“Gwamnati tana da bukatarku musamman kasancewar mafi yawanku sun karanta fannonin kiwon lafiya ne.
“Nan ba da jimawa ba za a tura ku asibitoci daban-daban domin fara aiki.” In ji gwamnan.
Gwamna ya kuma ja hankalin daliban, da su saka wannan abin alkhairi da aka yi musu ta hanyar tsayawa su yi aiki tukuru, kasancewar dukiyar al’umar jihar aka diba aka biya musu har suka Kai ga matsayin da suka cimma a yanzu.

Daliban sun kammala Digirinsu na biyu a Jami’ar Symbiosis dake Kasar India.
sun kuma bayyana godiyarsu bisa tagomashin da gwamnan ya yi musu.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ba kowannensu Naira 100,000 a yayin Biki shan ruwan.