Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da kafa kwamitin magance matsalar karancin wakilcin ƴan asalin Kano a daukar ma’aikata a hukumomin gwamnatin tarayya, kamfanoni masu zaman kansu da kungiyoyi.
An kaddamar da kwamitin ne a ofishin sakataren gwamnatin Kano, Umar Ibrahim, kamar yadda wata sanarwa ta bayyana ranar Alhamis.
Umar Ibrahim ya nuna damuwa kan yadda ake ci gaba da hana ƴan asalin Kano damar samun aiki, duk da cewa jihar ce mafi yawan jama’a a Najeriya.
Ya ce adadin matasan Kano da ke fama da rashin aikin yi ya yi yawa matuka, kuma ana kyautata zaton ya fi na kowacce jiha a Najeriya.
Umar Ibrahim ya bayyana cewa an zabi mambobin kwamitin cikin kulawa ta musamman, inda suka kunshi kwararru da ke da gogewa da kwarewa a fannin hidimar jama’a.
Kwamitin yana karkashin jagorancin Danyaro Yakasai, mai baiwa gwamna shawara na musamman kan tsare-tsare da ci gaban zamantakewa, yayin da Ibrahim Muhammad, mai baiwa gwamna shawara kan harkokin albarkatun dan Adam, ke matsayin mataimakin shugaba.
Ayyukan kwamitin sun hada da duba tsarin daukar ma’aikata a hukumomin tarayya, kamfanoni masu zaman kansu da kungiyoyin sa-kai da ke aiki a jihar Kano.
Haka kuma, kwamitin zai tantance yawan yan asalin Kano da ke aiki a wadannan hukumomi, ya tuntubi hukumomin da abin ya shafa kan ka’idojin daukar aiki, tare da hada kai da hukumar raba daidai domin tabbatar da adalci da bin dokokin da suka dace.
An baiwa kwamitin wa’adin mako hudu domin gabatar da rahotonsa.
