Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya kaddamar da rundunar tsaron unguwannin Kano ta Kano State Neighbour hood Watch Corps, a yayin bikin faretin kammala horo da aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha dake Kano.
Rundunar dai ta ƙunshi jami’ai dubu biyu da aka tura zuwa ƙananan hukumomi 44 na jihar, wadanda suka hadar da mata 130 da maza 1,870, domin ƙarfafa tsaro a matakin ƙasa da kuma taimakawa wajen tattara bayanan sirri.
Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta samar wa rundunar kayan aiki da suka haɗa da motoci kirar Hilux 88 da babura 440, domin yaki da laifuka kamar fashi da makami, shan miyagun ƙwayoyi da daba a birane da karkara.
Ya kuma shawarci jami’an rundunar da su kasance masu ladabi, gaskiya da jajircewa, yana mai jaddada cewa tsaro na daga cikin manyan abubuwan da gwamnatinsa ta bawa fifiko saboda muhimmancin sa a fuskar ci gaban tattalin arziki da walwalar al’umma.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Gwamnan jihar Katsina, Umar Dikko Radda, na yabawa da shirin tare da alkawarin hada kai da jihar Kano wajen magance rashin tsaro.
