Shugaba Bola Tinubu ya umarci Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima da ya jagoranci wata babbar tawagar gwamnatin tarayya zuwa Kano sakamakon mummunar gobara da ta afuku a Kasuwar Singer ranar Asabar.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin shugaban kasa Mista Bayo Onanuga, ya fitar ranar Lahadi a Abuja.
“Tawagar, za ta taso daga Abuja ranar Litinin, za kuma ta iso Kano da sakon ta’aziyyar shugaba Tinubu ga ‘yan kasuwar da kuma al’ummar Kano da suka yi asarar biliyoyin nairori a gobarar”. In ji sanarwar.
Gobarar, wadda rahotanni suka ce ta tashi ne ranar Asabar da yamma, kuma ta ci gaba har zuwa safiyar Lahadi, ta yi barnar dukiya mai tarin yawa a kasuwar.
Tinubu ya bayyana tashin hankalinsa kan yadda wannan lamari ya kasance karo har sau biyu gobarar na tashi a kasuwar a kasa da mako biyu.
Tawagar za ta kuma isar da tallafin kudi domin taimaka wa wadanda abin ya shafa da kuma tallafa wa gwammnatin jihar wajen gyara kasuwar cikin gaggawa.
‘Yan tawagar da za su zo, sun hada da Kakakin Majalisar Wakilai Tajudeen Abbas, da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin da Sanata Kawu Sumaila da Wakili Abubakar Kabir Bichi, Shugaban Kwamitin Kasafi na Majalisar Wakilai.
Sauran su ne Ministan Jin Kai, Dakta Bernard Doro da Shugabar Hukumar NEMA Malama Zubaida Umar.
Tun da farko, Shugaban ya tattauna ta wayar tarho da Gwamna Abba Kabir Yusuf domin samun bayani kan halin da ake ciki dangane da lamarin.
Tinubu ya kuma bayar da umarnin gudanar da bincike na tsanaki kan abubuwan da ke haddasa yawan gobarar kasuwanni.
